IQNA

17:11 - May 25, 2009
Lambar Labari: 1782645
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da taron juyayin rasuwar marigayi Ayatollah Ozma Muhammad Taqiyi Bahjat a birnin Islamabad fasar mulkin kasar Pakistan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Pakistan ya habarta cewa; An gudanar da taron juyayin rasuwar marigayi Ayatollah Ozma Muhammad Taqiyi Bahjat a birnin Islamabad fasar mulkin kasar Pakistan. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da taron a jami'ar Alkausar da ke birnin Islamabad, inda shugaban jami'ar da wasu manyan malamai na kasar suka halarta tare da gabatar da jawabai na ta'aziyya ga duniyar musulmi musamman ma mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah SAW. A lokacin da yake gabatar da nasa jawabi shugaban jami'ar Alkausar Sheikh Mohsen Najfi ya mika sakon ta'aziyya ga dukkanin al'ummar musulmi na duniya dangane da wannan babban rashi da duniyar musulmi ta yi, ya kuma bayyana kadan daga cikin tarihin rayuwar marigayin, wanda ya shahara da tsoron Allah da gudun duniya, da kyawawan dabi'u, da kuma koyi da iyalan gidan manzon Allah.

409980Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: