IQNA

14:55 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1805088
Bangaren kasa da kasa; An fassara littafin addu'ar nan mai suna Sahifa sajjadiyya wanda ya kunshi addu'oin Imam Zanul Abidin AS zuwa harshen Turkanci, wanda Abdlaziz Khatib Malamin jami'a a jamia'r birnin Marmar na kasar Turkiya ya fassara.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran haber 7 cewa; An fassara littafin addu'ar nan mai suna Sahifa sajjadiyya wanda ya kunshi addu'oin Imam Zanul Abidin AS zuwa harshen Turkanci, wanda Abdlaziz Khatib Malamin jami'a a jamia'r birnin Marmar na kasar Turkiya ya fassara. Bayanin ya ci gaba da cewa wanna karon farko da aka tarjama littafin sahifa sajjadiya zuwa harshen Turkanci, wanda kuma ko shakka babu hakan zai taimaka al'ummar kasar Turkiya wadanda bas u fahimtar harshen larabci wajen fahimtar hakikanin abin da addu'oin na cikin littafin sahifa sajjadiya suka kunsa. Malamin ya bayyana cewa tarjamar tana daya daga cikin abubuwan day a dauka wajibi ne ya yi domin kara fitowa da hasken iyalan gidan manzon Allah.
437327Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: