Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na birnin Tehran cewa; Wanda ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran ya bayyana cewa; hadin kai da sanin makiya shi ne babban abin day a hana makiya samun nasara kan tsarin mulunci na Iran. Bayanin ya ci gaba da cewa wanna shafin internet zai mayar da hankali wajen yada al'amurra da suka shafi addinin musulunci, tare da mayar da martani kan shubhohin da ake yi kana addinin musulunci, domin kuwa daga cikin dalilan bude wannan shafi har da isar da sakon addinin musulunci ga wadan dab a musulmi ba, domin sanin irin koyarawar addini da kuma bayyana musu hakikanin abin da ke tattare da wannan addinin sabanin abin da makiya musulunci suke nunawa a shafukan internet.
444398