Kamfanin dillancin labaran ikan ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut na kasar Labanan cewa; Malamin addinin nan na kasar Labanan kuma mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi'a na kasar labanan Sheikh Kabalan ya yi suka dangane da shiru da kasashen duniya ke yi kan laifukan Isra'ila. Sheikh Kabalan ya bayyana cewa kasashen duniya suna ganin irin ta'asar da Isra'ila take tafkawa a duniya amma sun gum da bakunansu, ina batun kare hakkokin mutane da al'ummomin duniya.
447153