Kamfanin dillancin labaran Iqna reshen birnin Kabul na kasar afganistan ya bayyana cewa; Shugaban majalisar malaman addinin musulunci a kasar Afganistan Maulawi Muhammad Shah ya bayyana bayyana cewa; makiyan al'ummar Afganistan na hankoron dushe hasken koyarwar kur'ani a tsakanin al'ummar Kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa kasashen yammacin turai suna kokarin ganin cewa bayan samun damar shiga cikin kasar kamar yadda suke fatan gani, suna nuna matukar damuwarsu dangane da tasirin kur'ani tsakanin al'ummar kasar. 468708