IQNA

Ordogon Ya Bukaci Duniya Ta Hadu Wajen Yaki Da Ta'addanci

17:04 - March 10, 2010
Lambar Labari: 1896737
Bangaren siyasa da zamantakewa; Rajib Taib Ordogon firaministan kasar Turkiya a cikin wani jawabi day a gabatar ya bukaci hadewa wajen yaki da ta'addanci.
Daga reshenta na kasar Turkiya bayan ta nakalto daga jaridar Alwatan ta Saudiya cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Rajib Taib Ordogon firaministan kasar Turkiya a cikin wani jawabi day a gabatar ya bukaci hadewa wajen yaki da ta'addanci.Firaministan kasar ta Turkiya ya jaddada cewa a yau duniya na bukatar hada kai da tuntubar juna wajen yaki da ta'addanci kuma shi ta'addanci ba shi da dangantaka da addini,ko al'umma don haka baki daya a tashi domin yakar wannan matsala.

550626

captcha