IQNA

Koyar Da Tafsirin Kur'ani Mai Tsarki A Birnin Damascus

20:26 - July 13, 2010
Lambar Labari: 1955268
Bangaren kur'ani; An fara aiwatar da wani shiri na share fagen koyar da tafsirin kur'ani mai tsarki a birnin Damascus na kasar Syria, wanda baki 'yan kasashen waje musamamn turkawa daga cikinsu suke halarta.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na bangaren hulda da jama'a na ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar Syria an habarta cewa, an fara aiwatar da wani shiri na share fagen koyar da tafsirin kur'ani mai tsarki a birnin Damascus na kasar Syria, wanda baki 'yan kasashen waje musamamn turkawa daga cikinsu suke halarta a wasu wurare na musamman da aka kebi domin hakan.

Bayanin ya ce dukkanin masu halartar shirin masana ne da suke gudanar da nazari a wasu fannoni na addini, daga cikin abin da shirin fara mayar da hankali a kansa shi ne koyar da su harshen larabci, wanda shi ne mabudin sanin tafsirin kur'ani mai tsarki.

An gayyaci wasu daga cikin malaman jami'oin kasar Turkiya domin su bayar da tasu gudunmawar wajen gudanar da wannan shiri, ta yadda zai samu nasara.

612859








captcha