IQNA

A watan Azumi Mai Girma A Turkiya Za A Samar Masallatan Tafi Da Gidanka

16:39 - July 20, 2010
Lambar Labari: 1959389
Bangaren kasa da kasa;Ali Baridak Uglu shugaban hukumar da ke kula da addini a kasar Turkiya ya watsa rahoton cewa; daga cikin shirye-shirye na musamman a watan azumi akwai kafa masallatan tafi da gidanka a cikin watan azumin ramadana mai albarka.


Cibiyar da ke kula harkokin kur;ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto gazetevatan ta watsa rahoton cewa; Ali Baridak Uglu shugaban hukumar da ke kula da addini a kasar Turkiya ya watsa rahoton cewa; daga cikin shirye-shirye na musamman a watan azumi akwai kafa masallatan tafi da gidanka a cikin watan azumin ramadana mai albarka. Baradak Uglu ya bayyana cewa samar da masallatan tafi da gidanka a wasu yankuna na kasar ta Turkiya zai taimaka ko shakka babu a daidai wannan lokaci na watan azumin ramadana kuma wannan wata hanya ce ko shakka babu da za ta kawo sauki ga musulmi a wannan wata na azumi mai tsarki.


617243
captcha