Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mataimakin ministan ma'aikatar kula da bunkasa harkokin al'du na Iran Hamid Muhammadi ya bayyana cewa sakon da jami'ar Almostafa (SAW) take dauke da shi ga al'ummar musulmi shi ne gina al'umma mai imani da koyarwar kur'ani mai tsarki a dukkanin bangarori na rayuwar dan adam.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin jami'an wannan makaranta a birnin Qom, inda ya tabbatar da hakan a zantawar da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran iqna yayin ziyarar tasa.
Ya ce hakika cibiyar tana gudanar da ayyuka masu matukar muhimmanci wajen yada manufofin kur'ani mai tsarki a duniyar musulmi, wanmda a cewarsa hakan babban abin alfahari ne ga musulmi baki daya.
622043