IQNA

Gasar Kur'ani Dole Ta Zama Dalilin Hadin Kan Al'ummar Musulmi

21:23 - July 29, 2010
Lambar Labari: 1963743
Bangaren kasa da kasa; Sarkin kasar Malazia Mizan Zainul abiding ya bayyana cewa gasar karatun kur'ani ta duniya da ake gudanarwa dole ne ta zama wani babban mafari na samun hadin kai tsakanin dukkanin al'ummar musulmi na duniya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin gudanar da tarukan bude gasar kur'ani ta kasa da kasa a birnin Kualalampor na kasar Malazia, sarkin kasar Mizan Zainul abiding ya bayyana cewa gasar karatun kur'ani ta duniya da ake gudanarwa dole ne ta zama wani babban mafari na samun hadin kai tsakanin dukkanin al'ummar musulmi na duniya baki daya.

Ya ci gaba da cewa kur'ani mai tsarki littafi na dukkanin musulmi baki daya, a kan haka dole ne musulmi su amfani da wannan dammar ta gudanar da gasar karatun wannan littafi mai tsarki domin samun hadin kai da fahimtar juna atsakaninsu.

Ya yaba da yadda musulmi suke bayar da muhimmanci matuka wajen harkokin gasar kur'ani a ko'ina cikin fadin duniya, ya yi lale maharbin ga dukkanin bakin da suke halartar gasar daga kasashe daban-daban.

622250



captcha