Hakim Firuz wanda ya halarci wannan gasa ta kasa da kasa ta Kur'ani a Malaisiya a lokacin wata tattaunawa day a yi dad an rahoton cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga Kalalampur ya bayyana cewa; wanda ya halarci gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a malaishiya tilawar karatun kur'ani mai kyau da murya mai dadi a irin wannan gasar ta Malaisiya na sawa mutane sha'awar karanta kur'ani da kokarin yin harda. Ya kara da jaddada cewa gudanar da irin wannan gasa wata babbar dama ce ko shakka babuta yada al'adar karantawa da hardar kur'ani saboda maharda da wadanda suka yi fice wajen tilawa da haradar Kur'ani daga kasashe daban-daban za su halarta inda kowa zai nuna kwarewarsa da salonsa.
623621