IQNA

A Karon Farko An Wallafa Da Watsa Mujallar Kur'ani Ta Kanuz A Palasdinu

12:16 - August 08, 2010
Lambar Labari: 1969028
Bangaren kasa da kasa; a karon farko an wallafa da watsa mujallar kur'ani ta Kanuz a Palasdinu da mu'assisar hardar kur'ani mai tsarki ta Alfurkan ta palsdinu ta watsa.


Gazi Isa shugaban yada labarai a panet.co.ib ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran cewa majiyar kusa da mu'assisar hardar kur'ani ta Furkan a Palasdinu ta bayyana masa cewa; a karon farko an wallafa da watsa mujallar kur'ani ta Kanuz a Palasdinu da mu'assisar hardar kur'ani mai tsarki ta Alfurkan ta palsdinu ta watsa.Wannan mujalla ko shakka babu ta yi bayanai masu gamsarwa da suka shafi harkokin kur'ani da yadda musulmi za su amfana da kuma bangarori da suka shafi rayuwar zamantakewa da kuma fannoni na rayuwa mai inganci.



627826

captcha