IQNA

Malaman Musulmi Na Duniya Za Su Nufi Yankin Gaza

11:52 - August 17, 2010
Lambar Labari: 1974936
Bangaren kasa da kasa; Shugaban kwamitin koli na malaman muslunci na kasa da kasa ya fadi cewa manayan malamai daga sassa daban-daban na kasashen musulmi za su nufi yankin zirin Gaza da nufin kawo karshen killacewar da haramtacciyar kasar Isra'ila take ya yankin.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar Syria an habarta cewa, Shugaban kwamitin koli na malaman muslunci na kasa da kasa ya fadi cewa manayan malamai daga sassa daban-daban na kasashen musulmi za su nufi yankin zirin Gaza da nufin kawo karshen killacewar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi wa yankin na tsawon shekaru.

Rahoton ya ce majalisar malaman ta fitar da bayani da ke cewa wajibi ne da ya rataya kan dukkanin musulmi su dauki matakan da suka kamata domin kawo karshen killace Gaza.

Shugaban kwamitin musulmin kasar Afirka ta kudu ya fadi cewa wasu daga cikin malaman addinin Musulunci na kasar na cikin shirin kama hanyar zirin Gaza.

634616











captcha