Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga garin dalmanhuras ta watsa rahoton cewa; a ranar juma'a ne ashirin da tara ga watan murdad na she karat a dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garen Nierdersachsen a lardin Barnam aka gudanar da taro karo na sha biyu na hukumomin hadin kai da na musulmi na Turkiya a Jamus . A gurin wannan taro an samu halartar wakilan irin wadannan kungiyoyi masu yawa inda suka tattauna da gudanar da bincike kan yadda za su binkasa ayyukansu da kuma yadda za su inganta ayyukansu a fadin kasar ta Turkiya.
637704