Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga Bernama ya watsa rahoton cewa; a yankin Malaka na kasar malaishiya ne a cikin wannan wata na azumin ramadana aka gudanar da karatun kur'ani na bai daya day an makaranta suka yi a cibiyar kasuwanci ta duniya a yankin.Kimanin yan makaranta dubu goma sha biyar ne yan shekaru goma da sha daya suka halarci wannan guri da kuma suka fito daga yankunan daban daban na kasar .Adadin da suka halarci wannan karatu a wannan karo yan zarta na baya da suka halarta da adadinsu ya tashi dubu goma sha uku da dari takwas da saba'in da bakwai.
638574