Bangaren kasa da kasa; a kasar Rasha ce za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma karo na goma sha daya kuma za a gudanar da wannan gasar ce a ranar lahadi biyu ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Masko fadar mulkin kasar ta Rasha.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Islam RF ya watsa rahoton cewa; a kasar Rasha ce za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma karo na goma sha daya kuma za a gudanar da wannan gasar ce a ranar lahadi biyu ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Masko fadar mulkin kasar ta Rasha. A wannan karo gasar ta shafi kira'ar kur'ani mai girma tare da taimakon komitin masu fitar da fatawa a kasar Rasha da kuma kungiyar hadin kan kasashen musulmi da hukumar Yunusko da tare da wakilan kasashen musulmi da wakilan musulmi mazauna kasashen dab a na musulmi ba.
641695