Mai kula da cibiyar ilimi da al'adu ta Kausar a Afganistan a wata tattaunawa day a yi da kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: A Afganistan an fara gaddamar da shirin sabkar karatun kur'ani mai girma a dalilin wannan wata mai alfurma a cikin kwanaki goma.Kuma wannan shiri an fara gaddamar da shi net un ranar farko ta watan azumin Ramadana a yankuna daban daban na kasar ta afganistan kuma a cikin kwanaki talatin sau uku za a sabke kur'ani mai girma a kasar.
645031