IQNA

An Girmama Masu Gudanar Da Gasar Kur'ani A Kasar Qatar

13:29 - October 18, 2010
Lambar Labari: 2015102
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani taro na girmama wasu makaranta kur'ani mai tsarki a kasar Qatar bayan da suka taka muhimmiyar rawa a gasar kur'ani da aka gudanar a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani lbari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Gulf Times cewa, an gudanar da wani taro na girmama wasu makaranta kur'ani mai tsarki a kasar Qatar bayan da suka taka muhimmiyar rawa a gasar kur'ani da aka gudanar a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro ya samu halartar manyan jami'ai daga ma'aikatar kula da ayyukan addini ta kasar, wadda ta dauki nauyin gudanar da wannan taro tare da hadin gwiwa da cibiyar bunkasa ayyukan kur'ani.

Daga cikin wadanda suka nuna kwazo a wanan gasa akwai wadanda suka karanta juzu'i na daya zuwa na biyar, kamar yadda wasu suka karanta har rabin kur'ani.

676589

captcha