Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Asesko ya watsa rahoton cewa; taron kasa da kasa kan koyar da kur'ani mai girma musamman ga masu koyarwa da kuma mahardata Kur'ani daga kasashen Turai a garin Zagrab babban birnin kasar Kurwasiya. Wannan taro da ake gudanarwa tun ranar alhamis ashirin da tara ga watan Mihr na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka fara gudanar da shi kuma an samu halartar makarantu ashirin da uku da mahardata da suka halarci wannan taro.
680314