Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga jaridar alnajaf Alyaum da ake bugawa a kasar Iraki ya watsa rahoton cewa; a ranar shida zuwa goma sha uku ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Najaf mai tsarki a kasuwar baje koli tta farko kuma a karon farko za nuna wani rubutaccen kur'ani na hannu da ake dangantawa da imam Ali (AS). Wannan kasuwar baje kolin lardin da hubbarin Imam (AS) a masallacin Umran bin Shahin da arewacin Hubbarin ne suka dauki dawainiya da nauyin gudanarwa.A wajen kasuwar baje kolin akwai abubuwa masu yawan gaske na rubuce-rubuce da zane-zane na hannu da za a nunawa masu bukata.
698981