IQNA

Zangon Musamman Na Karatun Kur'ani A Jami'o'in Iraki

15:52 - November 27, 2010
Lambar Labari: 2038311
Bangaren kasa da kasa; darul Kur'ani mai girma da ke karkashin ofishin da ke kula da hubbarin mai tsarki na Imam Huseini (AS) ya shirya wani zangon karatu na musamman na karatun kur'ani mai girma da sanin hukumce-hukumce a jami'o'in kasar Iraki.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Nun ya watsa rahoton cewa; darul Kur'ani mai girma da ke karkashin ofishin da ke kula da hubbarin mai tsarki na Imam Huseini (AS) ya shirya wani zangon karatu na musamman na karatun kur'ani mai girma da sanin hukumce-hukumce a jami'o'in kasar Iraki. Gudanar da irin wannan zangon karatun kur'ani na musamman zai taimaka matuka gaya wajen inganta bangaren ilimin kur'ani mai girma a fadin kasar ta Iraki da kuma hakan zai iya zama abin koyi a sauran kasashe na musulmi da jami'o'in kasashen musulmin.

701608

captcha