IQNA

Za A Tarjama Kur'ani Da Yaren Amaziganci Na Kasar Romaniya

11:46 - December 04, 2010
Lambar Labari: 2041644
Bangaren kasa da kasa;za atarjama kur'ani mai tsarki a yaren al'ummar Amaziganci da Haj Muhammad Taib masani musulmi dan kasar Aljeriya ya gudanar da kuma nan bad a jimawa ba za a nuna wa jama'a.





Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Liberte Algerie ya watsa rahoton cewa; za atarjama kur'ani mai tsarki a yaren al'ummar Amaziganci da Haj Muhammad Taib masani musulmi dan kasar Aljeriya ya gudanar da kuma nan bad a jimawa ba za a nuna wa jama'a. Kuma a halin yanzu wannan tarjamamman kur'ani yana a kasar Saudiya domin yi masa kyara na karshe Kuma mahukumtan Saudiyan sun gayyaci wanda ya yi wannan tarjama zuwa kasar domin ba shi kyauta ta musamman kan wannan jan aiki da ya gudanar da kuma jinjina masa kuma an ba shi kyauta ta musamman ta kasa .Suma musulmin kasar ta Aljeriya sun gudanar da zama na musamman tare da shi kan wannan jan aiki nasa.

705498


captcha