IQNA

An Bude Wata Makarantar Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Mauritania

14:05 - January 05, 2011
Lambar Labari: 2059546
Bangaren kasa da kasa, An bude wata makarantar kur’ani mai tsarki a birnin Nuakshut fadar mulkin kasar Mauritania, tare da hadin gwiwa tsakanin ofishin jakandancin kasar Gambia da kuma ma’aikatar kula d aharkokin addinin musulunci ta kasar mauritania.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na iqnq ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar faransa AFP an bayyana cewa, an bude wata makarantar kur’ani mai tsarki a birnin Nuakshut fadar mulkin kasar Mauritania, tare da hadin gwiwa tsakanin ofishin jakandancin kasar Gambia da kuma ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar mauritania da kan dauki nauyin shirya tarukan addini.

Wannan cibiya dai za ta mayar da hankali wajen shirya taruka na addinin muslunci da kuma gami da gasar karatu da hardar kur’ani ta kasashen yammacin nahiyar Afirka, haka nan kuma cibiyar ta kunshi ajujuwan koyar da karatu da harda, da kuma babban dakin gudanar da tarukan addinin muslunci.

Bude wannan makarantar kur’ani mai tsarki a birnin Nuakshut fadar mulkin kasar Mauritania, tare da hadin gwiwa tsakanin ofishin jakandancin kasar Gambia da kuma ma’aikatar kula d aharkokin addinin musulunci ta kasar mauritania baki daya zai taimaka ma harkokin kur’ani.
724161




captcha