IQNA

Shugaban Komitin Kasa Na Musulmin Filipine Ya Ziyarci Darul Kur'ani A Masallacin Maharlika

15:54 - January 16, 2011
Lambar Labari: 2065503
Bangaren harkokin kur'ani: a daidai lokacin gudanar da gasar karatun kur'ani a masallacin Maharalika ,shugaban komitin kasa na musulmin kasar Filipine ya ziyarci darul Kur'ani da ke cikin masallacin.



Kamfanin dillacin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a daidai lokacin gudanar da gasar karatun kur'ani a masallacin Maharalika ,shugaban komitin kasa na musulmin kasar Filipine ya ziyarci darul Kur'ani da ke cikin masallacin.Bayi Umar Lukman shugaban komitin kasa na musulmin kasar ta Filipine a lokacin wannan ziyarar tasa ya ja hankalin matasa da su maida himma wajen hardar kur'ani da kuma irin alfanon da ke tattare da hakan.


730655
captcha