Bangaren ayyukan kur'ani, An yaba da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Mashhad mai alfarma, wadda aka gudanar a matsayi na kasa da kasa, tare da halartar wakilai daga kashen duniya sama da arba'in.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da bayyana ra'ayoyi da malamai da masana ke ci gaba da yi gasar kur'ani a Iran, an yaba da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Mashhad mai alfarma, wadda aka gudanar a matsayi na kasa da kasa, tare da halartar wakilai daga kashen duniya sama da arba'in, da suka hada da kasashen larabawa da na musulmi.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da shugaban ofishin jagoran juyin juya halin muslunci bangaren isa da sakon addinin muslunci ya bayyana cewa, hakika an kyakkyawan daukar bakuncin gasar, wanda hakan ne ya kara fito da manufarta a idon duniya.
Ana dai ci gaba da yabawa da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Mashhad mai alfarma, wadda aka gudanar a matsayi na kasa da kasa, tare da halartar wakilai daga kashen duniya sama da arba'in na duniya.
732299