IQNA

Darul Qur'an" a Kano sun gabatar da gajeren Kwas a harabar cibiyar

11:26 - February 01, 2011
Lambar Labari: 2073852
A Karo na biyu sabuwar cibiyar Darul Quran da ke da mazauni daura da jami'ar Bayaro [BUK] Kano ta gabatar wani gajeren kwas ga Malaman makaratun Al-Kurani daga makaratun Fudiyoyi, makarantun Allo da na Islamiyya daga laraba 15- Jummaa zuwa 17 ga Safar
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa; A Karo na biyu sabuwar cibiyar Darul Quran da ke da mazauni daura da jami'ar Bayaro [BUK] Kano ta gabatar wani gajeren kwas ga Malaman makaratun Al-Kurani daga makaratun Fudiyoyi, makarantun Allo da na Islamiyya daga laraba 15- Jummaa zuwa 17 ga Safar 1432 (19-21/1/2011) a cibiyar.
Taken wannan kwas din shine “Karfafa masaniyar Malaman makarantun Al-Kurani, Islamiyoyi da na Allo” wanda Malam Yusuf Abdullahi ya gabatar da jawabi mai taken “Akhlaq na Al-Kurani”, Malam Auwal Shamsu, shi ma yayi nasa jawabin mai taken “Inganta makarantun Al-Kurani”, sai kuma Malam Muhammad Adis, da ya yi nasa jawabin mai taken “Muhimmancin harshen larabci wajen koyar da Al-Kurani," Malam Nura Lawan, ya yi akan “Kira’o’in Al-Kurani”, sai kuma Malam Abdul Razak, kan “Muhimman abubuwan lura ga Malamin Al-Kurani”.
Malam Sunusi Abdul Kadir Koki ya kasance babban bako mai rufe kwas din inda ya karfafi mahalarta wajen kokarinsu na inganta karatun da suke karantarwa yana mai jaddada mahimmanci Al-Kurani ga kowane Musulmi. Malamin bai gushe ba yana kara nanata wasiyyar Manzo (S) na riko ga nauyaya biyu, Al-Kurani da Ahlul Bait (AS).
Kaga ga duk wanda ke riko da Al-Kurani yana mai koyo da koyarwa yana mai hidima da kokarin yada daawah to dole ne ya zamo gogagge a wajen sanin Al-Kurani.
Mai kula da cibiyar a yayin zantawa da shi ya nuna cewa: domin riko da wasiyyar Manzo (S) cibiyar na kokarin shirya darussa da kwasa-kwasai domin riko da wasiccin Manzo (S).


739048

captcha