IQNA

Babban Taron Kasa Da Kasa Kan Kur'ani Da Addu'a A Birnin Qom

19:29 - February 02, 2011
Lambar Labari: 2074462
Bangaren kur'ani, Jami'ar Almostafa (SAW) da ke birnin Qom za ta shirya gudanar da wani babban taro mai taken kur'ani da addu'a a birnin a cikin shekara mai kamawa, wanda za a gudanar a mataki na kasa da kasa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da Hamid Reza Karimi jami'i mai kula da bangaren nazarin hadisi a sashin nazarin ilmomin kur'ani da hadisi na jami'ar Almostafa, ya bayyana cewa Jami'ar za ta shirya gudanar da wani babban taro mai taken kur'ani da addu'a a birnin a cikin shekara mai kamawa, wanda za a gudanar a mataki na kasa da kasa, da zai samu halartar masana.

Ya ci gaba da cewa an gudanar zaman tattauna yadda za a shirya taron da kuma yadda zai gudana a yau, inda dukkanin mambobin sashin nazarin ilmomin kur'ani da hadisi na jami'ar da aka gayyata suka bayar da irin shawarwarin da suke dauke da su kan hakan, inda za ayi dubi tare da daukar abubuwan da za a aiwatar a zama na gaba.

Bayanin ya ci gaba da cewa, jami'ar Almostafa (SAW) tana daya daga cikin jami'oi a kasar Iran da suke taka gagarumar rawa wajen yada ilmomin addinin Musulunci a matsayi na kasa da kasa, musamman ma a baya-bayan nan ta mayar da hanakali kan lamurra da suka danganci kur'ani mai tsarki.

740439
captcha