Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wali Ahmad wani karamin yaro baindiye dan shekaru goma sha biyu kacal a duniya a yankin Saharnipur na lardin Utarpuradash na kasar ta Indiya ya yi sa'ar hardace kur'ani mai girma.Wali Ahmad ya fara harder kur'ani mai girma a babbar makaranta ta Falah Darain da ke birnin kuma a ranar laraba da ta gabata hudu ga watan Isfand na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya yi sa'ar hadace kur'ani da fatar Allah ya daura mu kan damshinsa amin.
753101