IQNA

Jami'ar Musulunci Ta Kasar Burnai Za Ta Bude Bangaren Nazari Kan Ilmomin Kur'ani

13:10 - February 28, 2011
Lambar Labari: 2087490
Bangaren kasa da kasa, Jami'ar muslunci ta kasar Burnai za ta bude bangaren nazari kan Ilmomin kur'ani mai tsarki, da nufin kara bunkasa harkokin bincike kan bangarori na ilimi da ke cikinsa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Burnei Times an habarta cewa, Jami'ar muslunci ta kasar Burnai za ta bude bangaren nazari kan Ilmomin kur'ani mai tsarki, da nufin kara bunkasa harkokin bincike kan bangarori na ilimi da ke cikinsa ga wadanda suke da sha'awar gudanar da nazaria a wannan bangare.

Shugaban jami'ar Sultan Sharif da ake kasar ta Burnei Haji sarbini matahir shi ne ya sanar da hakan, inda ya sheda da cewa da yardarm Allah jamia'r za tya koma karatukanta a cikin wannan mako, kuma daga zangon karatu na gaba ne bangaren nazaarin ilmomin kur'anin zai fara gudanar da ayyukansa.

Wannan jami'ar muslunci ta kasar Burnai za ta bude bangaren nazari kan Ilmomin kur'ani mai tsarki, da nufin kara bunkasa harkokin bincike kan ilmomin kur'ani, domin bayar da dama ga masu bincike su fada nazarinsu.

754314



captcha