Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; a ranar bakwai ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a wani buki na musamman da aka gudanar a kasar Jodan aka nuna a fili wani kur'ani da aka fassara da yaren kuramai .Fassara wannan kur'ani da harshen da kowa yake Magana da shi musamman kuramai zai bas u damar sanin irin nasihohin da suka zo a cikin kur'ani mai girma da kuma hasken da ke cikinsa da hakan zai zama irshadi a cikinsa.
754419