IQNA

Tarjamar Kur’ani Zuwa Fitattun Harsunan Duniya Ya Zama Wajibi

13:11 - March 02, 2011
Lambar Labari: 2089272
Bangaren kur’ani, Limanin masallacin juma’a na birnin Borujard ya bayyana cewa, tarjama kur’ani mai tsarki zuwa wasu fitattun yaruka na duniya ya zama wajibi a halin yanzu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labaransa na Lorestan ya bayar da rahoton cewa, limanin masallacin juma’a na birnin Borujard ya bayyana cewa, tarjama kur’ani mai tsarki zuwa wasu fitattun yaruka na duniya ya zama wajibi a halin yanzu, bisa la’akari da yadda al’ummomin duniya da dama suke son su san abin da kur’ani mai tsarki ya kunsa.
Bayanin ya ci gaba da cewa malam Hassan Turabi ya nuna irin muhimmancin da ke tattare da tarjamar kur’ani zuwa wasu harsuna, yadda hakan kan taimaka matuka wajen isar da sakon kur’ani zuwa ga sauran al’ummomi cikin sauki, musamman ma wadandaharsunasu suka zama fitattu a duniya.
Ya kara da cewa ta hanayar tarjama kur’ani zuwa wasu harsuna na daban na daga cikin muhimman ayyukan da juyin juya halin musulunci Iran ya mayar da hanakali kansu, da nufin kara fafada masaniya kan kur’ani tsakanin al’ummomin duniya baki daya.
Limanin masallacin juma’a na birnin Borujard ya jaddada cewa, tarjama kur’ani mai tsarki zuwa wasu fitattun yaruka na duniya ya zama wajibi da ya kamata a mayar da hanakali kansa.
756197


captcha