Bangaren kasa da kasa, gamayyar jamiyun adawa na mabiya mazhabar shi’a kasar Bahrain suna kira zuwa ga kawo karshen mulkin mulukiyya na kasar tare da kafa tsari na jamhuriyya, da zai baiwa al’ummar kasar zabar shugaban kasa ta hanyar kada kuri’a.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari d aya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na al’alam an bayyana cewa, gamayyar jamiyun adawa na mabiya mazhabar shi’a kasar Bahrain suna kira zuwa ga kawo karshen mulkin mulukiyya na kasar tare da kafa tsari na jamhuriyya, da zai baiwa al’ummar kasar zabar shugaban kasa ta hanyar kada kuri’a maimakon yadda sarki shi ne wuka shi ne nama a cikin dikin dukkanin harkokin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa gamayyar kungiyoyin da kumajamiyun siyasar ta jaddada hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar da aka raba shi a lokacin gudanar da zanga-zangar neman sauyi, wadda ke ci gaba da gudana musamman a birnin Manama fadar mulkin kasar, inda dubban mutane suke ci gaba da yin gangami.
gamayyar jamiyun adawa na mabiya mazhabar shi’a kasar Bahrain suna kira zuwa ga kawo karshen mulkin mulukiyya na kasar tare da kafa tsari na jamhuriyya, da zai baiwa al’ummar kasar zabar shugaban kasa ta hanyar kada kuri’a.
760873