Bangaren kur’ani, an sanar da sunayen wadanda za su shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki da za a gudanar a kasar Sri Lanka, wadda za ta hada da karatu wato tilawa da kuma harda gami da kiran salla, wadda jami’ar Al-mostafa ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yada labaran yankin gabacin Asia cewa, an sanar da sunayen wadanda za su shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki da za a gudanar a kasar Sri Lanka, wadda za ta hada da karatu wato tilawa da kuma harda gami da kiran salla, wadda jami’ar Al-mostafa ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wannan mako.
Bayanin ya ci gaba da cewa reshen jami’ar al-mostafa ta kasa da kasa ne wato cibiyar ilimi ta manbaul huda ta dauki shirya gasar, yanzu haka dai sama mutane saba’in 70 suka yi rijistar sunayensu, da suka hada da masu manyan shekaru da kuma kanan shekaru.
an sanar da sunayen wadanda za su shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki da za a gudanar a kasar Sri Lanka, wadda za ta hada da karatu wato tilawa da kuma harda gami da kiran salla, wadda jami’ar Al-mostafa ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
760630