Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labarin da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-qods an habarta cewa, An bude wasu manyan cibiyoyin kula da harkokin kur'ani mai tsarki a sansanonin palastinawa 'yan gudun hijira da ke kasar Jordan, wanda cibiyar kula da ayyukan alkhairi ta kasashen musulmi ta bude, wanda ya bayar da dama ga palastinawa su yi hardar kur'ani cikin sauki.
A wani labarin kuma jami'an tsaron HKI sun killace yankin Aurata da ke gabacin birnin Nablus a gabar yamma da kogin Jordan, bayan halaka wasu yahudawan sahyuniya biyar da wasu da ake zaton palastinawa 'yan gwagwarmaya ne suka yi, a matsugunnan yahudawa na Itmar da ke kudu maso gabacin garin Nablus.
Sojojin HKI gami da 'yan sanda cikin shirin yaki, sun suna ta sintiri a yankin, haka nan kuma sun hana dukkanin palastinawa da ke yankin fita daga gidajensu. Wani bapalastine da ke cikin gidansa Abdulsalam Jamal, ya sheda wa wata kafar yada labarai ta wayar tarho cewa, sojin HKI na shirin aikata mummun ta'addanci ne kan al'ummar yankin, domin daukar fansa kan halaka yahudawan biyar da aka a kusa da yankin.
An kai harin ne kan yahudawan a lokacin da suke al'ummar yankin suke kokawa kan tsokanarsu da yahudawan suke yi, ta hanyar shiga yankunansu tare cin zarafinsu, wasu lokuta ma har da harbi da bindiga, ba tare mahukuntan HKI sun hana su ba.
762014