IQNA

An Ci Gaba Da Gudanar Da Wani baje Koli Na Zane-Zanen Kissoshin Kur’ani A Esfahan

15:16 - March 24, 2011
Lambar Labari: 2097926
Bangaren kur’ani, an fara gudanar da wani baje koli na zane-zane kan kissoshin kur’ani, da kuma bayani kan abubuwan da za su faru a ranar tashin alkiyama, ranar da dukkanin bayi za su hadu da ubangijinsu domin fuskantar hisabi kan ayyukansu na rayuwar duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto dag bangaren yada labaransa na lardin Esfahan an bayyana cewa, an fara gudanar da wani baje koli na zane-zane kan kissoshin kur’ani, da kuma bayani kan abubuwan da za su faru a ranar tashin alkiyama, ranar da dukkanin bayi za su hadu da ubangijinsu domin fuskantar hisabi kan ayyukansu na rayuwar duniya domin faakarwa ga al’ummar musulmi.
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki ta kasar an habarta cewa, za a gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki da ta kebanci jami’an tsaro a kasar Sudiyya, wadda za ta fara daga ranar Juma, kuma wannan shi ne karo na shida da ake gudanar da wannan gasa a birnin Makka mai alfarma.
A wani bangare kuma an bayyana cewa an dakatar da buka kur’ani mai tsarki a babbar cibiyar sarki Fahad da ke birnin Madina mai alfarma, wadda ita ita ce cibiya mafi girma da ke buga kwafin kur’ani a kasar Saudiya, sakamakon shiga yajin aiki da ma’aikatan cibiyar suka yi a cikin makon nan da muke ciki.
Bayanin ya ci gaba da cewa, Mahukuntan kasar Saudiyya sun yi iyakacin kokarinsu wajen ganain sun gamasar da ma’aikatan wannan cibiya domin kada suka shiga yajin aiki, amma kokarin bai haifar da da mai ido ba, inda daga karshe dai ma’aikatan suka shiga yajin aikin, wanda ya yi sanadiyar tsayawar dukkanin ayuukan cibiyar cak.
765982



captcha