Bangaren kur’ani, an sayar da kwafin kur’ani mai tsarki guda dubu 400 wadanda aka tarjama, lamarin da ke tabbatar da cewa mutane masu bukatar sanin ilimin kur’ani mai tsarki suna karuwa a kowane lokaci a tsakanin al’ummar musulmi da suke rayuwa a wannan zamani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an sayar da kwafin kur’ani mai tsarki guda dubu 400 wadanda aka tarjama, lamarin da ke tabbatar da cewa mutane masu bukatar sanin ilimin kur’ani mai tsarki suna karuwa a kowane lokaci a tsakanin al’ummar musulmi da suke rayuwa a wannan zamani na yau.
A bangare guda kuma bayanin ya yi nuni da cewa an gudanar da wannan zaman taro ne da nufin kara karfafa mabiya addinin musulunci kan sanin addininsu da kuma tarihin manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, wanda hakan ne zai ba su damar yin aiki da koyarwa a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwar zamantakewa.
An gudanar da wani zaman taro na mabiya addinin musulunci a yankin Rajuri na yankin keshmir, wanda ya samu halartar daruruwan malaman addini da kuma mutanen yankin wadanda akasarinsu mabiya addinin musulunci ne.
765833