Bangaren kur'ani, za a gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki da ta kebanci dakarun sama na jamhuriyar muslunci ta Iran, da za ta hada da matansu da kuma yaransu gami da su kansu, domin kara karfafa gwiwarsu kan harkokin kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The News an habarta cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Pakistan ya daukaka kara zuwa ga hukumar 'yan sanada ta kasa da kasa dangane da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu suka yi a kasar Amurka a cikin lokutan nan domin kaskantar da mabiya addinin muslunci.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ashararin mutum ya yi hakan ne domin kawo karshen duk wani zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinan kiristanci da na Musulunci da suke zaune lami lafiya a kasashe daban-daban na duniya, wanda hakan ke tabbatar da cewa akwai wata manufa da za ta amfanar da yahudawan sahyuniya ta karkashin kasa wajen yin hakan.
Shugabannin kasashen Turkiya da Pakistan sun yi Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka, wanda wani la'antacce da ke kiran kansa kirista ya yi domin tsokanar al'ummar musulmi a ko'ina.
ministan harkokin cikin gida na kasar Pakistan ya daukaka kara zuwa ga hukumar 'yan sanada ta kasa da kasa dangane da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu suka yi a kasar.
764252