IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taron Debe Kewa Da Kur'ani Da ya kebanci Sojoji

15:09 - April 03, 2011
Lambar Labari: 2099862
Bangaren kur'ani, babban jami'i mai kula da hulda da jama'a na rundunar sojin jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro da ya shafi debe kewa da kur'ani mai tsarki, da ya shafi jami'an soji na jamhuriyar muslunci, tare da halartar manyan hafsoshi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, babban jami'I mai kula da hulda da jama'a na rundunar sojin jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro da ya shafi debe kewa da kur'ani mai tsarki, da ya shafi jami'an soji na jamhuriyar muslunci, tare da halartar manyan hafsoshin sojin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa da dama daga cikin wadanda za su halarci wannan gasa suna da kyakkyawan horo da suka samu karatun kur'ani da kuma harda, bugu da kari kan hakan za a gudanar da zaman ne tare da gudanar da gasa, inda aka bayar da dama ga dukkanin mahalartan daga cikin sojojin su halarto da iyalansu da kuma bas u izinin shiga cikin gasar.

Babban jami'I mai kula da hulda da jama'a na rundunar sojin jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro da ya shafi debe kewa da kur'ani mai tsarki, da ya shafi jami'an soji na jamhuriyar muslunci, tare da halartar manyan hafsoshi.

760746




captcha