Bangaren kasa da kasa: shugaban sashen da ke kula da bangaren harkokin kur'ani mai girma da kuma da harkokin addini a kasar Koweiti ya bada labarin fara gasar kasa da kasa ta harda da karatun kur'ani da tajwidi n kur'ani mai girma na babbar kyauta a Koweiti daga ranar ashirin da hudu ga watan Farvardin na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.