Bangaren kasa da kasa; dubban yan kasar Afganistan ne a ranar talatar da ta gabata sha shidda ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in suka ci gaba da gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da tofin Allah tsine da kona kur';ani da wani malamin coci ya yi a kasar Amerika a wani mataki na haddasa rikici da tashin hankali.