Bangaren kasa da kasa;a wani taron manema labarai na hadin guiwa tsakanin kasashen Malaishiya da jamhuriyar musulunci dangane da ilimi jami'a a tsakanin kasashen biyu wato Iran da Malaishiya inda a wannan taron ne kasar ta Malaishiya ta bayyana a shirye take ta yi aiki kafada da kafada tare da jamhuriyar musulunci ta Iran ta fuskar harkokin Kur'ani.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a wani taron manema labarai na hadin guiwa tsakanin kasashen Malaishiya da jamhuriyar musulunci dangane da ilimi jami'a a tsakanin kasashen biyu wato Iran da Malaishiya inda a wannan taron ne kasar ta Malaishiya ta bayyana a shirye take ta yi aiki kafada da kafada tare da jamhuriyar musulunci ta Iran ta fuskar harkokin Kur'ani.Kasashen biyu dai sun yi rawar gain ta fuskar yadawa da binkasa ilimi musamman ilimin addini da harkokin kur'ani mai girma kuma wannan mataki ko shakka babu zai taimaka matuka gaya da kuma ciyar da harkokin kur'ani a gaba.
769832