Bangaren kur’ani, an gudanar da wani zaman taro da ya yi dubi kan matsyin kur’ani mai tsarki da kuma sunnar ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa ta fuskacin mu’ujiza, wanda aka gudanar a karo na uku a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrwa na yanar gizo na post jordan an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro da ya yi dubi kan matsyin kur’ani mai tsarki da kuma sunnar ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa ta fuskacin mu’ujiza, wanda aka gudanar a karo na uku a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar ta Jordan musamman daga birnin na Aman.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai yi dubi kan hanyoyin da ya kamata a bi domin saka hannayen jari wanda hakan zai iya habbaka dukkanin bangarori na yawon shakatawa da bude a cikin kasashen musulmi, musamman idan aka yi la’akari da irin muhimmancin da wannan bangare yake da shi a cikin kasashen musulmi.
Za a gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan nazari dangane da kare hakkokin daliban makarantun addinin muslunci a kasar Thailand, wanda hakan zai bayar da damar sanin halin da suke ciki da yadda ake kare hakkokinsu a bangaren ilimi da abin da ya yi kama da hakan na karatu.
774465