IQNA

Musulman Cana Sun Yi Tuni Da Shekara Tarjama Kurt'anin Farko Da Cananci

14:30 - April 23, 2011
Lambar Labari: 2110423
Banagaren kasa da kasa; musulmi a kasar Cana sun yi tuni da cika shekaru talatin cir da tarjamawa da kuma watsa tarjamar littafin kur'ani mai girma na farko a cikin harshen Cananci da Allama Muhammad Makin ya yi kuma a dalilin zagayowar wannan rana sun yi buki na musamman.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; ; musulmi a kasar Cana sun yi tuni da cika shekaru talatin cir da tarjamawa da kuma watsa tarjamar littafin kur'ani mai girma na farko a cikin harshen Cananci da Allama Muhammad Makin ya yi kuma a dalilin zagayowar wannan rana sun yi buki na musamman. A shekara ta dubu daya da dari tara da shida miladiya aka haifi Muhammad Makin a lardin Shadiyan na kasar Cana kuma yana cikin na farko-farko daga cikin wadanda suka yi kokowa da rawar ganin an kyautata al'adun musulmi a kasar ta Cana kuma ya kamala karatunsa ne a jami'ar Azhar ta kasar Masar kuma ya kafa daya daga cikin manyan cibiyoyin addini a kasar Cana. Kuma a shekara ta dubu daya da dari tara da tamanin da daya ne ya fassara kalmomi da mafahimul kur'ani a cikin harshen Cananci.

778606

captcha