IQNA

Kungiyoyin Musulmi Na Ci Gaba Da Sukar Mahukuntan Bahrain Kan Kone Kur'ani

14:29 - April 23, 2011
Lambar Labari: 2110434
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyi da dama a kasashen dniya na ci gaba da yin tofin Allah tsine kan keta alfarmar kur'ani da mahukuntan kasar Bahrain suka yi tare da hadin gwiwa da gidan sarautar kasar Saudiyya, kamar yadda suke keta alfarmar wuraren ibada da suka hada da masallatrai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, kungiyoyi da dama a kasashen dniya na ci gaba da yin tofin Allah tsine kan keta alfarmar kur'ani da mahukuntan kasar Bahrain suka yi tare da hadin gwiwa da gidan sarautar kasar Saudiyya, kamar yadda suke keta alfarmar wuraren ibada da suka hada da masallatan kasar.

Bayanin ya ci da cewa akasarin mutanen da suka rusa masallatai wadanda suke cikin jami'an tsar one ko kuma suke samun kariya daga jami'an tsaron, bayan da mahukunta suka ba su umurnin su yi hakan, kuma da dama daga cikinsu ba mutanen asali ba ne na kasar Bahrain, kuma bayan sanar da sunayensu duniya za ta gani, tare da hotunansu a lokacin da suke tafka wannan ta'asa.

Za a fitar da sunayen dukkanin wadanda suke da hannu kai tsaye wajen rusa masallatai da wuraren ibada da kuma kone kur'ani mai tsarki a kasar Bahrain, bisa la'akari da musun da mahukuntan kasar suka yi dangane da wadanda aka ambata cewa suna da hannu wajen rusa masallatai a kasar.

778668
captcha