IQNA

Wata Majami'a A kasar Amurka Ta Rarraba Kur'anai A Jahar Yutai

14:29 - April 23, 2011
Lambar Labari: 2110435
Bangaren kas ada kasa, wata majami'ar mabiya addinin kirista a kasar Amurka ta rarraba kur'ani mai tsarki ga mutane kyauta, domin sanin addinin muslunci da kuma samun fahimtar juna tsakanin mabiya addinin kirista da kuma musulmi, ta yadda hakan zai kawar rashin fahimtar juna samakon ayyukan wasu daga bangarorin biyu.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sltrib an bayyana cewa, wata majami'ar mabiya addinin kirista a kasar Amurka ta rarraba kur'ani mai tsarki ga mutane kyauta, domin sanin addinin muslunci da kuma samun fahimtar juna tsakanin mabiya addinin kirista da kuma musulmi, ta yadda hakan zai kawar rashin fahimtar juna samakon ayyukan wasu daga bangarorin biyu na mabiya dukkanin addinan.

Wannan rahoto ya kara da cewa mabiya addinai daban-daban na kasar Amurka sun nuna rashin amincewarsu da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu mabiya addinin kirista suka yi a kasar da sunan yunkurin bayyana ra'ayinsu, wanda ake ganin hakan wani aiki ne na tsokana ga al'ummar musulmi na kasar Amurka da sauran kasashen duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai wasu daga cikin mabiya addinin kirista da suke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan lamari, wanda mabiya addinan suke ganin cewa idan ba a dauki matakan kawo karshen hakan ba, za a iya fadawa cikin wani mawuyacin hali tsakanin dukkanin al'immomin duniya.

778642


captcha