IQNA

Mata Musulmi Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Faransa Domin Kin Amincewa Da Tozarta Su

21:00 - May 02, 2011
Lambar Labari: 2116132
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mata musulmi ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Montravi domin nuna rashin amincewarsu da cin fuska da suke fuskanta sakamakon saka hijibin musulunci da suke yi, sun gudanar da jerin gwanon ne domin nuna wa mahukuntan kasar irin matsalolin da suke fusknata daga masu gaba da addinin muslunci a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na atlasinfo an bayyana cewa, daruruwan mata musulmi ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Montravi domin nuna rashin amincewarsu da cin fuska da suke fuskanta sakamakon saka hijibin musulunci da suke yi, sun gudanar da jerin gwanon ne domin nuna wa mahukuntan kasar irin matsalolin da suke fusknata daga masu gaba da addinin muslunci a kasar ta Faransa.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Faransa na daga cikin kasashen turai da suke da mabiya addinin muslunci da dama, amma saboda tasirantuwa da da gwamnatin kasar ta yi daga shiftar yahudawan sahyuniya, ana nuna ma musulmi banbanci a cikin lamurra da dama, da hakan ya hada da shi kansa shugaban kasar, wanda ya shahara da kin addinin muslunci.
Daruruwan mata musulmi ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Montravi domin nuna rashin amincewarsu da cin fuska da suke fuskanta sakamakon saka hijibin musulunci da suke yi, sun gudanar da jerin gwanon ne domin nuna wa mahukuntan kasar irin matsalolin da suke fusknata daga masu gaba da addinin muslunci a kasar. 784303

captcha