Bangaren kasa da kasa, babban malamin mai bayar da fatawa akasar Auzbakistan sheikh Usman Alimuff ya bayyana cewa, masu koyon fasahar rubutun hannu a babbar cibiyar koyon rubutu da zane-zane ta birnin Tashkend fadar mulkin kasar suna yin amfani da rubutun kur’ani domin samun gogewa da fasahar rubutu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar dar alhayat an bayyanac ewa, babban malamin mai bayar da fatawa akasar Auzbakistan sheikh Usman Alimuff ya bayyana cewa, masu koyon fasahar rubutun hannu a babbar cibiyar koyon rubutu da zane-zane ta birnin Tashkend fadar mulkin kasar suna yin amfani da rubutun kur’ani domin samun gogewa da fasahar rubutu ta wannan hanya.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nasij kuma an bayyana cewa, za aguudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan mu’ujizar ilimin kur’ani mia tsarki da kuma sunnar manzon Allah (SAW) wanda za agudanar a karo na goma a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar masana daga sassa na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro an sabar gudanar da shi a kasar ta Turkiya, wanda ma’aikatar kula da ayyukan addinin musuluci ta kasar ta kan dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kowace shekara, tun daga shekara ta dubu biyu da daya da ta gabata, inda masana kan gabatar da laccoci da kuma makalolin da suka tanada kan hakan.
785623