Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da shari'ar mutumin nan mai cin zarafin musulmi da hanayar keta alfarmar kur'ani mai girma, bayan da kotu ta ki yarda ta kore shari'ar kamar yadda masu ra'ayinsa gami da masu goyon bayansa daga cikin jami'an gwamnatin kasar suka nema.
Kamfanin dillancin labarn iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, ana ci gaba da shari'ar mutumin nan mai cin zarafin musulmi da hanayar keta alfarmar kur'ani mai girma, bayan da kotu ta ki yarda ta kore shari'ar kamar yadda masu ra'ayinsa gami da masu goyon bayansa daga cikin jami'an gwamnatin kasar suka nema daga kotun.
a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar saudiyya an bayyana cewa, babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ya bayyana cewa za abude wata bababr cibiyar kula da bincike da nazari kan tarihin manzon Allah (SAW) a birnin Jidda na kasar, domin bayar da dama ga masu bincike su kara fadada ayyukansu ta wannan fuska, musamman bisa la'akari da muhimmancin da ke tattare da hakan.
Wasu bayanan sun tabbatar da cewa, tun bayan da ma'aikatar kula da ayyukan addinin ta kasar saudiyya ta bayyana hakan, da dama daga cikin masana da manazarta sun bayyana cewa hakan zai taimaka musu matuka, matukar dai za a samar da littafai na sahihin tarihi wanda ba agurbata ba, ko saka ra'ayi na bangaranci da nufin tallata wata akida tasa.
797601