IQNA

Za A Gudanar Da Taron Girmama Mahardata Da Makaranta Kur'ani Na Kasar Qatar

14:47 - May 25, 2011
Lambar Labari: 2128500
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro na girmama mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki na kasar Qatar da suka taka rawa da kuma nuna kwazo a lokacin gasar kur'ani ta kasar, inda za a ba su kyautuka na musamman a gaban taron.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na na kamafanin dillancin labaran kasar Qatar cewa, za a gudanar da wani zaman taro na girmama mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki na kasar Qatar da suka taka rawa da kuma nuna kwazo a lokacin gasar kur'ani ta kasar, inda za a ba su kyautuka na musamman a gaban taron da zai samu halartar masana.

Wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar saudiyya an bayyana cewa, babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ya bayyana cewa za abude wata bababr cibiyar kula da bincike da nazari kan tarihin manzon Allah (SAW) a birnin Jidda na kasar, domin bayar da dama ga masu bincike su kara fadada ayyukansu ta wannan fuska, musamman bisa la'akari da muhimmancin da ke tattare da hakan.

Wasu bayanan sun tabbatar da cewa, tun bayan da ma'aikatar kula da ayyukan addinin ta kasar saudiyya ta bayyana hakan, da dama daga cikin masana da manazarta sun bayyana cewa hakan zai taimaka musu matuka, matukar dai za a samar da littafai na sahihin tarihi wanda ba agurbata ba, ko saka ra'ayi na bangaranci da nufin tallata wata akida ta daban.

797530
captcha