IQNA

Taron Girmama Matan Da Suka Lashe Gasar Karatun Kur'ani A Gambiya

12:48 - May 26, 2011
Lambar Labari: 2128784
Bangaren harkokin kur'ani : an gudanar da bukin kamala gasar karatun kur'ani da kuma bukin girmama matan da suka yi sa'ar cin nasara a wannan gasar karatun Kur'ani mai girma a jamhuriyar Gambiya da kuma aka gudanar a ranar talatin da daya ga watan Urdebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma a fadar shugaban kasa ne a ka gudanar da wannan bukin girmamawa. A birnin Banjul.



Kamfanin dillancin labarai na ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; an gudanar da bukin kamala gasar karatun kur'ani da kuma bukin girmama matan da suka yi sa'ar cin nasara a wannan gasar karatun Kur'ani mai girma a jamhuriyar Gambiya da kuma aka gudanar a ranar talatin da daya ga watan Urdebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma a fadar shugaban kasa ne a ka gudanar da wannan bukin girmamawa. A birnin Banjul.A gurin wannan bukin girmama matan da suka lashe wannan gasar karatun kur'ani mai girma an samu halartar mamyan malaman addini da ministan ilimi na kasar wanda ya yi jawabi kan rawa da muhimmanci da kuma tasirin mata a tarihin musulunci da cewa ya zama wajibi a ilmantar da musulmi koyarwar musulunci da sirar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.

798343

captcha